Home Labaru Sabbin Nade-Nade: Mele Kyari Ya Zama Sabon Shugaban Kamfanin NNPC

Sabbin Nade-Nade: Mele Kyari Ya Zama Sabon Shugaban Kamfanin NNPC

339
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada Mele Kolo Kyari a matsayin sabon shugaban kamfanin mai na NNPC.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Ndu Ughamadu ta fitar, ta ce Shugaba Buhari ya nada wasu sabbin shugabannin bangarorin kamfanin guda bakwai.

Kafin wannan nadi dai, Mele Kyari ya taba rike mukamin wakilin Nijeriya a Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin cewa, Mele da sauran sabbin shugabannin bangarorin za su yi aiki ne tare da masu rike da mukamin na da, har sai ranar 7 ga watan Yuli na shekara ta 2019, don tabbatar da cewa an mika aikin ba tare da wata tangarda ba.