Home Labaru Bincike: ICPC Ta Fara Bibiyar Yadda ‘Yan Majalisu Ke Kashe Kudaden Ayyukan...

Bincike: ICPC Ta Fara Bibiyar Yadda ‘Yan Majalisu Ke Kashe Kudaden Ayyukan Mazabun Su

211
0

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin zarkin kasa zagon kasa
ICPC ta ce ta fara bincike domin gano yadda ‘yan majalisu da
‘yan kwangila ke kashe kudaden ayyukan mazabu da gwamnati
ta ba su.
Shugaban hukumar Farfesa Bolaji Owasanoye ya bayyana haka
a ranar Talatar 2 da ta gabata a lokacin kaddamar da kwamitin
bin diddigin ayyukan mazabu da ‘yan majalisu ke gudanarwa a
Abuja.

Farfesa Owasanoye ya ce, za su tilasta wa duk dan kwangilar da
aka samu da laifin kashe kudaden kwangilar ta hanyar da bata
dace ba kammala ayyukan mazabun, ko kuma su dawo da
kudaden da suka handame, sannan a buga sunayen su a jaridu
tare da gurfanar da su gaban kotu.
Haka kuma Owosanoye ya ce sun hada kai da cibiyar masana
gine-gine ta kasa domin ta duba yanayin ayyukan mazabu da
‘yan majalisu suka yi, domin tabbatar da ko sun cancanci
kudaden da aka kashe wajen gudanar da su.
Daga karshe shugaban hukumar ta ICPC ya ce, matukar suka
samu nasara a wannan aikin da suka sa a gaba, tabbas ‘yan
Nijeriya zai samu sauki, sakamakon hukumomin yaki da
rashawa za su gudanar da aikin su yadda ya kamata.