Home Labaru Rashawa: An Nemi Shugaba Buhari Da Ya Dakatar Da Binciken Ibrahim Magu

Rashawa: An Nemi Shugaba Buhari Da Ya Dakatar Da Binciken Ibrahim Magu

290
0

Wasu Kungiyoyi sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da binciken da ake yi wa tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Wadannan kungiyoyi sun bukaci Muhammadu Buhari da ya yi fatali da kwamitin Ayo Salami da aka kafa domin ya binciki zargin da ake yiwa Ibrahim Magu, saboda zai yi  wuya ayi wa Magu adalci.

Kungiyoyin sun ce an dauki lokaci mai tsawo da sunan ana binciken tsohon shugaban hukumar EFCC ba tare da an gano gaskiyar komai ba.

Saboda haka ne kungiyoyin suka nemi gwamnatin tarayya ta wargaza kwamitin Ayo Salami domin Najeriya ta guji yin abin kunya a gida da gaban Duniya.

A cewar kungiyoyin, ba su adawa da binciken hukumar EFCC, sai dai tsoron su shi ne, tun farko an nuna kwamitin ba zai yi gaskiya a wajen wannan bincike ba.

Leave a Reply