Home Labaru Kalubale: Sanata Ndume Ya Ce Buhari Ya Na Zagaye Da Manyan Barayi...

Kalubale: Sanata Ndume Ya Ce Buhari Ya Na Zagaye Da Manyan Barayi A Mulkin Sa

139
0

Dan majalisar dattawa Sanata Ali Ndume, ya ce da yawa daga cikin wadanda ke karkasin shugaba Muhammadu Buhari barayi ne.

Sanata Ali Ndume ya sanar da haka ne, yayin wata hira da gidan Talabijin na Channels ya  yi dashi, inda ya ce akwai mutanen da ke kokarin ganin bayan ci-gaba a mulkin shugaba Buhari.

Dangane da yadda mulkin APC ke tafiya, Ndume ya ce ba ya farin ciki da tafiyar ta tsawon shekaru biyar, domin duk da su na yin iyakar kokarin su, amma akwai gurabe da dama da ya kamata a cike.

Ya ce shugaba Buhari sai dai ya bada umarni, amma ba zai iya zuwa ya yi ayyuka da kan sa ba, don haka mafi yawan matsalolin daga masu yin ayyukan ne.

Sanatan ya bada misali da yadda shugaba Buhari ya amince da biyan naira biliyan Dari 5 domin sama wa mutane ayyukan yi, musamman wadanda suka gama karatu kan fanin koyarwa, amma yawanci ba a dauka ba.