Jami’an rundunar atisayen Accord sun kashe wasu ƴan bindiga, tare da kama wasu da ake zargi da kuma kwace makamai a Jihar Katsina.
Lokacin misayar wutar, an kasha uku daga cikin ƴan bindigar, inda wasu daga cikinsu suka tsere da munanan raunuka sanadiyyar harbin bindiga.
An samu nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK47 guda 3 lokacin da aka yi misayar wuta daga hannun miyagun. Rundunar, ta ce tana kokari wajen ganin ta magance muggan laifuka a arewa maso yamma na Najeriya.














































