Home Labaru Oduduwa: Kotu Ta Umarci Gwamnati Ta Biya Igboho Diyyar Naira Biliyan 20

Oduduwa: Kotu Ta Umarci Gwamnati Ta Biya Igboho Diyyar Naira Biliyan 20

155
0
Sunday

Wata babbar kotu da ke birnin Badun a jihar Oyo, ta umarci gwamnatin tarayya ta ba Sunday Igboho naira biliyan 20, a matsayin diyyar barnar da jami’an tsaro na farin kaya DSS su ka yi ma shi yayin wani sumame da su ka kai gidan sa.

Tuni dai Sunday Igboho ya na hannun hukumomin jamhuriyar Benin, tun bayan tserewar da aka yi ma shi lokacin da jami’an na hukumar DSS su ka dira a gidan sa.

Bayan Sunday Igboho ya tsere ne, lauyoyin sa su ka maka hukumar DSS da ministan shari’a kotu, inda su ka nemi a biya shi makudan kudade saboda take hakkin sa na dan kasa.

Alkalin kotun dai ya umarci a biya Igboho Naira Biliyan 20 a matsayin diyya, kasa da abin da lauyoyin sa su ka nema tun da farko.

Leave a Reply