Home Labaru ‘Yan Ta’addan Da Ke Tserewa Daga Zamfara Sun Kafa Tuta A Kauyukan...

‘Yan Ta’addan Da Ke Tserewa Daga Zamfara Sun Kafa Tuta A Kauyukan Kaduna Biyu

704
0
Bandits Flag

‘Yan Ta’adda da sojoji ke ci-gaba da fatattaka daga jihar Zamfara, yanzu haka sun mamaye garuruwan Saulawa da Damari da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa manema labarai cewa, daruruwan ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan kungiyar Ansaru ne sun isa garuruwan biyu, sannan daga baya su ka kafa tutoci a kauyukan Damari da Saulawa.

Damari da Saulawa dai su na daga cikin ƙauyukan da ‘yan ta’adda su ka mamaye ba tare da kasancewar jami’an tsaro ba.

Majiyoyi sun ce, a ‘yan shekarun da su ka gabata, garuruwan biyu sun kulla yarjejeniya da ‘yan bindiga domin a ba su damar yin noma, yayin da aka ba ‘yan ta’addan damar shiga kasuwanni da sauran abubuwan more rayuwa a cikin garuruwan.

Sai dai majiyar ta ce, daga bisani yarjejeniyar ta lalace a cikin watan Fabrairu, a lokacin da ‘yan bindiga su ka mamaye garuruwa da dama ciki har da Saulawa da Damari su ka kashe mutane da dama.