Home Labaru Buhari Ya Yi Abin Da Komawa APC Ne Kawai Zan Yi In...

Buhari Ya Yi Abin Da Komawa APC Ne Kawai Zan Yi In Saka Masa – Fani Kayode

9
0

Tsohon ministan Sufuri kuma jigo a jam’iyyar PDP a da, Femi Fani-Kayode, ya bayyana komawar sa jam’iyyar APC da cewa ita kadai ce hanyar da iya saka wa irin Nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samu.

A jawabin da ya yi wa manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja,  Kayode ya ce ya koma jam’iyyar APC ne don ya hada hannu da gwamnatin shugaba Buhari a ciyar da Nijeriya gaba.

Ya ce shugaba Buhari ya taka rawar gani a Nijeriya, musamman a fannin harkar samar da tsaro.

Fani-Kayode, ya ce ita siyasa da ma haka ta gada, duk inda mutum ya ga nan ne ci-gaba ya karkata zuwa can idan har dan kishin kasa ne na gaske.

Gwamnan jihar Yobe Mala Buni, ya ce shugaba Buhari ya yi matukar Farin ciki a kan wannan gagagumin kamu da jam’iyyar  APC ta yi.