Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Belin Peter Obi Daga Hannun Birtaniya

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Belin Peter Obi Daga Hannun Birtaniya

109
0
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, ya ce jami’ai sun tsare, tare da hantarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peter Obi a birnin London.

Gwamnatin Tarayya, ta musunta labarin da ke cewa ta shiga
tsakani a kan tsare dan takarar shugaban kasa na jami’yyar
Labour Peter Obi da aka yi a Birtaniya.

Idan dai ba a manta ba, an tsare Peter Obi na dan wani lokaci a filin jirgin saman Hearthrow da ke London, bisa rashin gane ko shi wanene bayan ya je kasar domin gudanar da bikin Easter.

A ranar Alhamis da ta gabata ne, wani hoton bogi ya karade kafafen sada zumunta, inda ya nuna shugabar hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasar waje Abike Dabiri-Erewa zaune a wani ofis tare da Peter Obi da wani jami’in tsaron Birtaniya domin neman karbar belin sa.

Sai dai mai shugaban sashen yada labarai kuma kakakin hukumar Abdur-Rahman Balogun ya musunta labarin, inda ya ce Dabiri-Erewa ba ta je Birtaniya ba, kuma ba ta da hurumin neman belin kowane dan Nijeriya da ake zargi da aikata laifi a Birtaniya.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na Twitter, mai taimaka wa shugaban kasa a kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad, ya nesanta gwamnatin tarayya da neman belin Peter Obi bayan tsare shin da jami’an tsaro su ka yi a Birtaniya.

Leave a Reply