Home Labaru Sojoji Sun Rufe Gidajen Da Ake Lalata Da Yara Kanana a Maiduguri

Sojoji Sun Rufe Gidajen Da Ake Lalata Da Yara Kanana a Maiduguri

81
0

Rahotanni daga jihar Borno na cewa, sojoji sun kai samame a
kan rukunin gidajen mata masu zaman kan su da ke Kasuwar
Fara a unguwar Shagari Low-Cost, inda ake fasikanci da yara
masu karancin shekaru.

Bayanai sun ce, yankin da jami’an tsaron su ka kai wa samamen, ya yi kaurin suna wajen hada-hadar mata masu kananan shekaru, wadanda su ka rungumi karuwanci a matsayin sana’a.

Ana kyautata zaton cewa, matakin sojoji na rufe rukunin gidajen Kasuwar Fara, ya biyo bayan rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa a kan badakalar da ke wakana a yankin, musamman yadda lamarin ya shafi mata masu kananan shekaru.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa, jami’an tsaron da su ka kai samamen sun kama wani adadin mutanen da ake zargin su na da hannu wajen barnar da ake aikatawa, inda su ka kara da cewa matakin ya tilasta daukewar kafa a yankin tamkar ba inda kasuwa ke ci ba.

Leave a Reply