Home Labarai Kotu Ta Sake Turawa Rarara Sammaci Kan Taurin Biyan Bashi a Kano

Kotu Ta Sake Turawa Rarara Sammaci Kan Taurin Biyan Bashi a Kano

320
0

Wata babbar kotun shari’ar addinin Musulunci da ke Kano, ta
bada umarnin sake rubuta wa shahararren mawakin jam’iyyar
APC Dauda Adamu Kahutu Rarara sabuwar takardar sammaci
saboda kin mutunta gayyatar ta.

Kotun, wadda ke zama a unguwar Rijiyar Zaki da ke birnin Kano a karkashin Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya ce ta bada umarnin yayin zaman ta na ranar Talatar da ta gabata.

Ana dai maka Rarara kotu ne bisa kin biyan kudaden wasu wayoyin salula da ya ke karba ya na raba wa mutane daga hannun wani dan kasuwa mai suna Muhammad Ma’aji, wadanda yawan su ya kai kimanin Naira miliyan goma da dubu dari uku.

Lauyan mai kara Barista I. Imam ya shaida wa kotun cewa, wanda ake karar bai mutunta sammacin da aka kai ma shi ba saboda kin halartar zaman kotun, sannan ya roki kotun ta bada umarnin a kamo Rarara saboda ya raina kotu.

Sai dai alkalin ya ce, kasancewar wanda ake tuhuma bai zo ba kuma bai aiko ba, kotun ta yi ma shi uzuri saboda wannan ne karo na farko da ya yi haka, daga nan ya bada umarnin a sake rubuta wa Rarara sabon sammaci a kai masa, ko kuma a lika a kofar gidan sa da ke kan titin gidan Zoo a Kano tare da

Leave a Reply