Home Labaru Matsayin Digiri: Sanata Shehu Sani Ya Maida Wa Shugaba Buhari Martani

Matsayin Digiri: Sanata Shehu Sani Ya Maida Wa Shugaba Buhari Martani

756
0
Sanata Shehu Sani, Dan Majalisar Dattawa

Dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya tofa albarkacin bakin sa a kan maganar da shugaba Buhari ya yi game da mallakar shaidar karatu ta Digiri.

Shehu Sani, ya ce yaran talakawa ne su ke wahalar samun aiki a Nijeriya, domin har gobe akwai shafaffu da mai wato yaran manya da samun aiki ya ke zuwa masu a cikin ruwan sanyi.

Sanatan, ya na maida martani ne a kan kalaman shugaba Buhari, inda ya ce a halin yanzu Digiri ba shi ke nuna tabbacin mutum zai samu aiki a Nijeriya ba.A wani jawabi da wallafa a shafin san a Twiter, Shehu Sani ya ce Digirin da ba a iya sama wa mutum abin yi da shi a Nijeriya shi ne wanda yaron Talaka ya yi, amma ya ce yaran masu hannu da shuni sun a samun aiki.

Leave a Reply