Home Labaru Martani: Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Ciwo Bashi Daga Kasar China –...

Martani: Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Ciwo Bashi Daga Kasar China – Amaechi

314
0
Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, ya ce Nijeriya ba ta ba kasar China jinginar manyan kadarori kamar tashoshin jiragen ruwa kafin ta ciwo bashi daga kasar ba.

Amaechi ya bayyana haka ne, a wajen taron Harkokin Sufuri na Afrika ta Gabas da aka gudanar a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Bayanin ministan dai ya biyo bayan rahotannin da ke cewa kasashen Sri Lanka, da Sudan, da Somalia da Kenya, sai da su ka bada jinginar tashoshin jiragen ruwa kafin kasar China ta jibga masu basussukan da su ka kasa biya.

Amaechi ya ce babu wata sarkakiya tsakanin kasashen Nijeriya da China, domin bashin da Nijeriya ta ciwo ba mai wahalar biya ba ne, kuma babu wata yarjejeniyar damka masu kadara a matsayin jingina kafin a karbi bashin.

Ministan ya kuma nuna cewa, basussukan da wasu kasashe su ka ci suka kasa biya a China, ya na shafar kokarin da Nijeriya ke yi idan ta je neman bashi a Chana. Ya ce shi ya sa su ke karakainar zuwa China, saboda ita kadai ce kasar da za ta bada bashi domin gina abubuwan inganta rayuwar jama’a.

Leave a Reply