Home Labaru Waiwaye: Buhari Ya Koka Da Zaman Da Aka Yi Tsakanin Bangaren Zartarwa...

Waiwaye: Buhari Ya Koka Da Zaman Da Aka Yi Tsakanin Bangaren Zartarwa Da Majalisa

288
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci game rashin jituwar da aka yi ta samu tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki ta tarayya, ya na mai cewa an yi mugun zama da juna kuma bai ji dadin hakan ba.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya gayyaci Sanata Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara domin buda baki tare da shi a fadar sa da ke Abuja.

Sanata Bukola Saraki ya bayyana wa shugaba Buhari cewa, a shirye majalisa ta ke a kowane lokaci wajen yi wa kasa hidima, don haka ya ce ba su da wata matsala daga bangaren su.Wadanda su ka halarci shan ruwan kuwa sun hada da Yakubu Dogara da Sanata Ike Ekweremadu, da Yusuf Lasun Sanata Ahmad Lawan, da Femi Gbajabiamila shugabannin masara rinjaye da mataimakan su.

Leave a Reply