Home Labaru Kiwon Lafiya Mata Dubu 800 Na Rayuwa Da Cutar Yoyon Fitsari a Najeriya- Rahoto

Mata Dubu 800 Na Rayuwa Da Cutar Yoyon Fitsari a Najeriya- Rahoto

80
0

Asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya, ya
ce akwai sama da mata dubu 800 da ke rayuwa da cutar yoyon
fitsari da kaso mai yawa a arewacin Nijeriya.

Da ya ke jawabi yayin yaye mata 50 da su ka warke daga cutar, Shugaban ofishin asusun reshen jihar Adamawa Dr Danladi Idrissa, ya ce fiye da rabin masu kamuwa da lalurar yoyon fitsari na arewacin Nijerya ya na da nasaba da al’adun al’ummar yankin.

Dr Idrissa ya kara da cewa, mata 225 daga cikin 265 da aka yiwa aikin yoyon fitsari sun warke garau karkashin jagorancin asusun da gidauniyar Fistula tare da hadin gwiwar ma’aikatar kula da harkokin mata ta Nijeriya.

Masana kiwon lafiya dai su na alakanta cutar yoyon fitsari da auren wuri, baya ga doguwar nakuda a gida, dalilan da ake ganin su ne kan gaba wajen haddasa lalurar.

Leave a Reply