Asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya, ya
ce akwai sama da mata dubu 800 da ke rayuwa da cutar yoyon
fitsari da kaso mai yawa a arewacin Nijeriya.
Da ya ke jawabi yayin yaye mata 50 da su ka warke daga
cutar, Shugaban ofishin asusun reshen jihar Adamawa Dr
Danladi Idrissa, ya ce fiye da rabin masu kamuwa da lalurar
yoyon fitsari na arewacin Nijerya ya na da nasaba da al’adun
al’ummar yankin.
Dr Idrissa ya kara da cewa, mata 225 daga cikin 265 da aka
yiwa aikin yoyon fitsari sun warke garau karkashin jagorancin
asusun da gidauniyar Fistula tare da hadin gwiwar ma’aikatar
kula da harkokin mata ta Nijeriya.
Masana kiwon lafiya dai su na alakanta cutar yoyon fitsari da
auren wuri, baya ga doguwar nakuda a gida, dalilan da ake
ganin su ne kan gaba wajen haddasa lalurar.
You must log in to post a comment.