Home Labarai Apc Za Ta Kalubalanci Nasarar Abba Gida-Gida a Kotu

Apc Za Ta Kalubalanci Nasarar Abba Gida-Gida a Kotu

1
0
Kotu ta bada umarnin a tsare Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas, tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin barazanar kisa.

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, ta shigar da kara a gaban
Kotun Sauraren korafe-Korafen Zabe ta jihar, ta na
kalubalantar zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga
watan Maris.

Mai magana da yawun jam’iyyar APC Ahmed Aruwa ya sanar da haka a Kano, inda ya ce jam’iyyar ta shigar da korafin ta ne ta na karar Hukumar Zabe ta Kasa da kuma Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano.

Jam’iyyar APC, ta ce sanar da sakamakon zaben da hukumar zabe ta yi ya saba da Dokar Zabe, duba da cewa an tafka kura- kurai a cikin sa.

Tuni dai jam’iyyar ta shigar da korafin a gaban kotun, wanda su ka ba masana shari’a na jam’iyyar umarnin shigewa gaba a shari’ar