Home Labaru Madalla: Sojojin Najeriya Sun Bankado Wani Mugun Shiri Da Boko Haram Ta...

Madalla: Sojojin Najeriya Sun Bankado Wani Mugun Shiri Da Boko Haram Ta Yi A Borno

1464
0
Sojan Najeriya
Sojan Najeriya

Dakarun rundunar Sojan Najeriya sun bankado tare da lalata wani shiri da kungiyar Boko Haram ta yi a jihar Borno, inda ta tura mayakanta domin su sa bama-bamai cikin ramukan kan hanyar Maiduguri zuwa Konduga da Bama.

Rundunar ta bayyana haka ta bakin mai magana da yawunta a rundunar ta 7, Kanal Ado Isa, ya ce ‘yan ta’addan sun binne bama-bamai tare da sauran ababen fashewa ne a ramukan kan hanyar da Sojoji ke wucewa da kayan aiki, a wani salon yaki.

Sai dai Sojojin sun bankado wannan shiri, inda rundunar ta aika da kwararrun Sojoji masu kwance bama-bamai zuwa babbar hanyar, inda suka kwance bama baman, sannan ta nemi jama’a mazauna yankin suka hadu su ciccike ramukan kan titin ta yadda motoci za su iya wucewa lafiya cikin sauki.

 Babban kwamandan runduna ta 7 ya yi kira ga Sojoji su kasance cikin azama tare da jajircewa domin ganin sun hana yan ta’adda walwala a yankin.

Leave a Reply