Home Labaru Kotu Ta Ba Hukumar AMCON Damar Karbe Kadarorin Donald Duke

Kotu Ta Ba Hukumar AMCON Damar Karbe Kadarorin Donald Duke

221
0

Babban kotun tarayya da ke Legas ta bada izni ga hukumar kula da kadarorin Najeriya wato AMCON ta karbe wata kadara da tsohon gwamnan Cross Rivers Donald Duke ya mallaka.

Mai shari’a Chuka Obiozor, ne ya bada dama ga hukumar ta dawo da wasu kadarori da Donald Duke, ya mallaka a Ikoyi da ke Legas hannun ta saboda tarin bashi.

Mai shari’a Chuka ya ce ana bin tsohon gwamnan da mai dakin sa Owanari Bob Duke, bashin kudi da yawan su ya kai naira miliyan 537 da dubu dari  334, da sunan wani kamfanin mai suna Stonehedge Investment Limited.

Wannan ya sa hukumar AMCON ta dumfari kotu a cikin farkon watan Agusta, inda ta ke neman a dawo da kadarorin da tsohon gwamnan ya mallaka.

Hukumra ta AMCON ta fadawa kotu cewae Donald Duke, ya bada gidan sa dake titin Temple, a Ikoyi da sunan jingina a lokacin da zai karbi bashin da yanzu ya gaza biya.

Hukumar ta roki kotu ta dakatar da kudin da ke cikin asusun bankin Donald Duke, da mai dakinsa da kamfanin su, har zuwa lokacin da aka karkare bincike.