Shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya Muhammad Abubakar Adamu, ya karbi bakuncin kasashe 194 wadanda ke cikin kungiyar ‘yan sanda ta kasa da kasa wadda aka fi sani da INTERPOL a Abuja.
Karanta wannan: Rashin Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Tabbatar Da Goyon Bayan Sa Ga Kwamitin Zamfara
Wannan shi ne karo na farko da za’a gudanar da taro irin wannan a yammacin Afirka, sannan kuma taron na zuwa ne a daidai lokacin da yankin ke fama da karuwar ta’addanci da kashe-kashen ‘yan bindigada da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba, ya ce shugaban rundunar zai gabatar da jawabi akan matsalolin tsaron da ke aukuwa a tsakanin kan iyakar kasa da kasa.
Ya ce shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya Muhammad Abubakar Adamu, shi ne zai kasance mutum na farko da ya fara karbar bakuncin taron kungiyar INTERPOL a Najeriya.
Bugu da kari, taron zai
samu halartar sauran hukumomin gwamnati wadanda suka hada da hukumar EFCC da
hukumar NDLEA da hukumar gyara halaye ta Najeriya da hukumar yaki da fasa
kwabri da hukumar yaki da safarar bil’adama da kuma hukumar NAFDAC.
You must log in to post a comment.