Home Labaru Ma’aikatar Shari’a Ta Sallami Alkalan Kotun Shari’a Biyu A Jihar Borno

Ma’aikatar Shari’a Ta Sallami Alkalan Kotun Shari’a Biyu A Jihar Borno

4
0

Hukumar kula da sashen shari’a ta jihar Borno, ta sanar da sallamar wasu Alkalan kotun shari’a guda biyu.

Wannan, na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, kuma Sakatarenta S.K Jidda ya rattafa wa hannu a Maiduguri.

Jidda ya ce, an yanke wannan shawarar ne a zaman da hukumar ta gudanar, inda ta tabbatar da sallamar Alkalin babbar kotu, Alkali Yakub.

Wannan dai ya biyo bayan binciken da aka gudanar ne bayan kararsa da kungiyar ci-gaban Kwayam ta kai ofishin shugaban Alkalai.

Shugaban Alkalan, ya mika karar ne zuwa kwamitin amsa korafe-korafe, inda aka gano cewa an yi amfani da Alkalin wajen cin zarafi.

Haka kuma, an salami Alkalin kotun Shari’a, Alkali El-Hassan, sakamakon samunsa da laifin zama a kotun da ba huruminsa ba.