Home Labaru Ana Rade-Radin Tsohon Ministan Buhari Ya Tara Naira Biliyan 9.7 A Lokacin...

Ana Rade-Radin Tsohon Ministan Buhari Ya Tara Naira Biliyan 9.7 A Lokacin Da Yake Ofis

19
0

Tsohon ministan man fetur, Ibe Emmanuel Kachikwu ya karyata zargin cewa ya tara Naira biliyan 9 da miliyan 700 a asusunsa yayinda yake rike da mukaminsa.

Emmanuel Kachikwu, ya rubuta takardar korafi ta hannun lauyansa Johnmary Jideobi zuwa ga Ministan shari’a Abubakar Malami, yana mai karyata zargin da ake yi masa.

Barista Johnmary Jideobi, ya ce wasu ne suke neman bata sunan Ibe Emmanuel Kachikwu kawai saboda bukatar kansu.

Wata jaridar yanar gizo, ta zargi Ibe Kachikwu da mallakar wata mota da aka sato daga kamfanin Jaguar a kasar Birtaniya, inda aka kai ta California a kasar Amurka.