Home Labaru Leken Asiri: An Yi Kutse A Wayar Ministar Leken Asiri A Afirka...

Leken Asiri: An Yi Kutse A Wayar Ministar Leken Asiri A Afirka Ta Kudu

489
0
Leken Asiri: An Yi Kutse A Wayar Ministar Leken Asiri A Afirka Ta Kudu
Leken Asiri: An Yi Kutse A Wayar Ministar Leken Asiri A Afirka Ta Kudu

Rahotanni sun ce an yi kutse a wayoyin ministar leken asiri a Afirka ta kudu, Ayanda Dlodlo, da mataimakinta Zizi Kodwa.

Masu bincike na duba ta yadda aka yi kutse a wayoyin su da kuma wayoyin wasu jami’an leken asiri, a cewar ma’aikatar tsaron kasar.

Sai dai babu masaniya kan wanda yake da hannu a lamarin ko kuma an yi kutse kan mahimman bayanai, in ji ma’aikatar.

Mai magana da yawun Dlodlo, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an gano kutsen lokacin da mutane da dama suka ga sakon karta-kwana daga Kodwa.

Lamarin dai na zuwa ne ‘yan makonni bayan an kutsa cikin shelkwatar hukumar tsaron kasar da ke Pretoria babban birnin kasar.

Barayi sun shiga wajen ajiyar mahimman bayanai a ofishin tare da tafiya da wasu takardu da kudade da ba a san yawan su ba kamar yadda aka wallafa a shafin IOL da ke intanet.

Leave a Reply