Wasu ‘yan majalisun dokokin Jamus daga jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi, sun shigar da karar Shugabar Gwamnatin Kasar, Angela Merkel, da ministocin ta bisa zargin su da hannu a kisan da Amurka ta yi wa Kwamandan sojin Iran, Qasem Soleimani.
Karar da ‘yan majalisun suka shigar na da nasaba da sansanin sojin Amurka da ke yammacin Jamus, inda ake kyautata zaton cewa, Amurka ta kafa tauraron dan adam a wannan sansani domin kula da jiragen ta mara matuka a sararin samaniyar nahiyar Afrika da kuma yankin gabas ta tsakiya.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, daya daga cikin ‘yan jam’iyyar ta masu tsattsauran ra’ayi, Alexander Neu, ya ce, a wannan sansanin na Rasmstein aka sarrafa hanyar sadarwar jirgi mara matukin da ya kaddamar da harin da ya yi sanadin mutuwar Soleimani na Iran.
A cikin watan Janairun da ya gabata ne, harin jirgin mara matuki ya hallaka Soleimani a Iraqi, lamarin da ya kusan haddasa yaki tsakanin Amurka da Iran .
‘Yan adawar na zargin Angela Merkel da ministocinta na harkokin waje da na tsaro da na cikin gida da wasu mambobin gwamnatin ta da taimakawa cikin sakaci har aka kashe kwamandan sojin na Iran.
You must log in to post a comment.