Home Labaru Kiwon Lafiya Zazzabin Lassa: Mutum 118 Sun Mutu A Najeriya

Zazzabin Lassa: Mutum 118 Sun Mutu A Najeriya

403
0
Zazzabin Lassa: Mutum 118 Sun Mutu A Najeriya
Zazzabin Lassa: Mutum 118 Sun Mutu A Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon barkewar cutar zazzabin Lassa daga farkon shekarar nan ya karu zuwa 118.

Hukumar ta bayyana haka cikin rahoton da take fitarwa kan halin da ake ciki game da cutar a       Najeriya.

Ta ce rahoton daga 1 ga Janairu zuwa 23 ga Fabrairun bana ne.

Akalla mutum 2,633 ne ake zargi sun kamu da Lassa tun farkon 2020 daga cikin su mutum 689 aka tabbatar sun kamu da cutar.

Mutanen sun fito ne daga kananan hukumomi 115 a jihohi 27 na Najeriya.