Home Labaru Kwamandan yaki da kungiyar Boko Haram Manjo Janar Benson Akinruloyu

Kwamandan yaki da kungiyar Boko Haram Manjo Janar Benson Akinruloyu

567
0

Rundunar sojin Nijeriya ta kwashe al’umomin kauyen Sabon-gari da ke karamar hukumar Damboa ta jihar Borno, inda ta ke mayar da su sansanin ‘yan gudun hijira da ke Damboa sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.

Kwamandan yaki da kungiyar Boko Haram Manjo Janar Benson Akinruloyu ya sanar da haka ga manema labarai, sannan ya ce daga safiyar Talata zuwa yammacin ranar, sojoji sun kwashe mutanen kauyen da dama zuwa sansanin ‘yan gudun hijira da ke Damboa.

Idan dai za a iya tunawa, ko a farkon watan Afrilun da ya gabata, sojoji sun kwashe daukacin al’ummar kauyen Jakana da ke da nisan kilomita 20 zuwa birnin Maiduguri a, inda suka sauya musu matsuguni domin tsiratadda su daga hare-haren ‘yan ta’addan Boko-Haram.

Leave a Reply