Home Labaru Ilimi Yada Labarai: An Shawarci Gwamnati Ta Dau Mataki Kan Kafafen Sada Zumunta-Almuhiyi

Yada Labarai: An Shawarci Gwamnati Ta Dau Mataki Kan Kafafen Sada Zumunta-Almuhiyi

317
0

Fitaccen malamin addinin musulunci Sheikh Muhammad Nasir Abdul Almuhiyi ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki mataki a kan kafafen sadarwa na zamanai ta hanyar kafa cibiya da za ta rika kula da yadda ake amfani da kafar.

Shiekh Abdul Almuhiyi wadda shine shugaban harkokin mulki na kungiyar Jama”atul Izalatul Bidi’a na kasa reshen Jos ya yi wannan kirar ne, yayin da ya jagoranci wata tawagar ‘yan kungiyar zuwa ofishin kungiyar ‘yan jarida na kasa NUJ reshen jihar Kebbi.

Ya ce idan gwamnati na son tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a Nijeriya, ya zama dole a sa ido a kan yadda ake amfani da kafafen sadarwa na zamani ta hanyar kafa wata hukuma da za ta rika kula da lamarin.

Sheikh Almuhiyi ya ce sun kai ziyara sakatariyar ‘yan jaridun ne domin kara dangon zumunci da kuma samun goyon baya, sannan ya shawarci manema labarai su guji wallafa labaran da za su iya janyo tashin hankali da tabarbarewar tsaro a Nijeriya.

A nashi jawabin shugaban kungiyar ‘yan jaridu na jihar Aliyu Jajirma ya ce, ziyarar ta zo a lokacin da ya dace kuma sun dauki darussa matuka gaya.