Jam’iyyar PDP ta ce matsalar tsaro da ake fama da ita a fadin Nijeriya bata rasa nasaba da yadda gwamnatin tarayya ta ke gabatar da mulkin ta.
Sakataren jam’iyyar na kasa Sanata Umaru Tsauri ya bayyana hakan ga manema labarai a wata zantawa da ya yi da su, inda ya kara da cewa, rashin bayyanawa al’’umma gaskiyar abinda ke faruwa yi shine ummul aba’isin abinda ya jefa Nijeriya cikin halin rashin tsaro.
Umaru Tsauri ya ce alhakin gwamnati ne ta gano mutanen da suke da hannu a matsalar tsaro, ba wai al’ummar kasa ne za su gano mata ba.
Sanatan ya kuma ce, halin da Nijeriya ta ke ciki, su kan su ‘yan adawa suna cikin damuwa matuka, saboda matsala ce da ta shafi kowa da kowa.
A karshe ya ce, mafita daya ce, gwamnati ta binciko masu hannu a cikin matsalar tsaro, sannan ta yarda cewa matsalace babba, kuma ta nemi mafita ta hanyar amfani da taimakon manyan mutanen da ke cikin gwamnati.