Home Labaru Kiwon Lafiya Kula Da Lafiya: Rashin Likitoci A Najeriya Ba Matsalaba Ce – Chris...

Kula Da Lafiya: Rashin Likitoci A Najeriya Ba Matsalaba Ce – Chris Ngige

669
0
Chris Ngige, Ministan kwadago Da Samar Da Ayyuka
Chris Ngige, Ministan kwadago Da Samar Da Ayyuka

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige, ya ce babu damuwa game da yadda likitocin Najeriya ke kaura zuwa kasashen waje domin neman ayyukan yi.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ake gabatar da wani shiri mai suna Sunrise Daily a gidan talabijin na Channels.

Chris Ngige, ya ce  babu damuwa saboda Najeriya na da likitoci fiye da yadda ake bukata, kuma idan akwai adadin likitoci haka, za ka iya barin likitoci su bar Najeriya ba tare da wata matsala ba.

Sai dai kungiyar likitoci ta Najeriya ta musanta bayanan ministan, inda ta ce akwai karancin likitoci a fannin kiwon lafiya.

Shugaban kungiyar Dokta Adedayo Faduyile, ya kalubanci ministan, inda ya ce duk da cewa shi ma ministan tsohon likita ne, yau she rabonsa da ya duba marasa lafiya. Dokta Adedayo, ya ce ya kamata ne a ce likita guda ya rika duba mutum 600, amma sabanin hakan yanzu a Najeriya likita daya na duba mutum 6,000 ne, wanda hakan ke kawo babban koma baya ga bangaren kula da lafiya.

Leave a Reply