Home Labaru Ziyara: Shugaba Buhari Zai Tafi London A Yau

Ziyara: Shugaba Buhari Zai Tafi London A Yau

310
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Birtaniya bayan ya kammala ziyara a birnin Maiduguri na jihar Borno a yau.

Mai maitamakawa shugaban kasa a kafafen yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ana sa ran shugaban kasa zai kaddamar da wasu ayyukan ci gaban al’umma musamman a bangaren ilimi da kiwon lafiya da kuma hanyoyi a ziyarar da zai kai jihar Borno.

Wasu rahotanni sun nuna cewar a lokacin ziyarar shugaban kasa a London, zai yi nazari game da sabbin ministocin da zai yi aiki da su a sabuwar gwamnatin sa. Rahotannin sun bayyana cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari  zai  dawo Najeriya ne a ranar 5 ga watan Mayu.