Home Labaru Rikicin Adamawa Da Taraba: Buhari Ya Bada Umarnin Kai Dauki

Rikicin Adamawa Da Taraba: Buhari Ya Bada Umarnin Kai Dauki

364
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a gaggauta kai dauki a yankunan da kashe-kashe da kone-kone ya shafa a jihohin Adamawa da Taraba.

Shugaban tawagar kai dauki, kuma babban daraktan bincike na hukumar agajin gaggawa ta kasa Akube Iyawu, bayyana haka, bayan ya  isa Yola na jihar Adamawa domin daukan mataki kan umarnin shugaban kasa.

A lokacin da yake magana a Fadar Hamman Bata da Hamman Bachama a Demsa da Numan, Akube Iyawu, ya ce sun je yankunan ne domin tantance asarar da aka yi ta rayuka da dukiyoyin jama’a a yankunan da rikice-rikicen suka yi kamari.

Ya ce wadanda rikicin ya shafa su saurari isowar kayan agaji daga gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NEMA nan ba da dadewa ba, sannan kuma ya mika ta’aziyyar shugaban kasa ga wadanda lamarin ya shafa. A na su jawabai, Stephen Rmiya na Bachama da Alhamdu Teneke na Bata, sun nuna godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tuna da su a cikin wannan mawuyacin hali, inda suka bukaci gwamnati ta gano hanyoyin da za ta kawo karshen fitintinu a cikin yankunan al’ummar su.

Leave a Reply