Home Labaru Kudin Binne Gawa: Tsohon Gwamnan Bauchi Ya Musanta Zargin Kashe Naira Biliyan...

Kudin Binne Gawa: Tsohon Gwamnan Bauchi Ya Musanta Zargin Kashe Naira Biliyan 2.3

569
0

Tsohon gwamnan jihar Bauchi Abubakar Mohammed, ya ce Naira biliyan 1 da miliyan 200 kacal ya kashe wajen sayen kayayyakin binne gawa ba Naira biliyan 2 da miliyan 300 da ake ikirari ba.

Mai taimaka wa tsohon gwamnan ta fuskar yada labarai Mukhtar jibril, ya ce tsohon gwamnan ya gaji al’adar sayen kayan jana’iza ne daga magabatan shi saboda mahimmancin da aikin ke da shi ga al’umma.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed dai ya tuhumi tsohon gwamnan da kashe Naira biliyan 2 da miliyan 300 wajen sayen kayan binne gawarwaki a cikin watanni biyar.

Jibril ya kara da cewa, an sayi kayan binne gawarwakin a kan ka’ida, kuma ‘yan kwangila nagari aka ba aikin sayen kayayyakin. A karshe ya bukaci al’ummomin jihar Bauchi su yi watsi da wannan labara na kanzon-kurege, wandda ya bayyana a matsayin ayyukan marasa kishin al’umma.

Leave a Reply