Home Labaru Sakamakon Canji: Abubuwa 5 Da Kungiyar Yarbawa Ta Roki Shugaba Buhari

Sakamakon Canji: Abubuwa 5 Da Kungiyar Yarbawa Ta Roki Shugaba Buhari

614
0

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere sun mika kokon barar abubuwa biyar da su ke bukata daga shugaba Muhammadu Buhari, inda su ka ce  matukar an samar da su za su taimaka wajen rage kalubalen da Nijeriya ke fuskanta.

Daga cikin abubuwan da kungiyar ke nema dai  akwai bukatar daukar kwararan matakan magance matsalolin tsaro a Nijeriya, tare da bada shawarar cewa, daukar ‘yan sanda daga kananan hukumomi 774 da ke fadin Nijeriya zai taimaka kwarai da gaske.

Sauran bukatun sun hada da samar da ilimi kyauta wanda kuma ya ke wajibi, da sama wa  matasa abin yi, da hadin kan kasa, da kuma inganta bangaren lantarki.

A na shi jawabin, shugaba Muhammadu Buhari ya ce za su duba bukatun kamar yadda ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe. Daga cikin mahalarta taron dai akwai Bola Ahmed Tinubu da Segun Osoba da Abiola Ajimobi da Sanata Adebayo Adeyeye, da Cif Kemi Nelson, da Laoye Tomori, da Solomon Akindele, da Elder Yemi Alade, da sauran su.