Home Labaru Kudin Shiga: Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Jami’an Hukumar ‘RMAFC’ A Abuja

Kudin Shiga: Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Jami’an Hukumar ‘RMAFC’ A Abuja

300
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da shugaba da kwamishinonin hukumar tattarawa da kasafta kudaden shiga ta tarayya a fadar sa da ke Abuja.

An dai fara taron rantsar da jami’an ne ne da misalin karfe 12:00 na rana a zauren fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Hukumar dai an kafa ta domin kula da shige da ficen kudade daga asusun tarayya, tare da yin nazari a kan dabarun rabe-raben kudaden shiga da kuma tsarin aiki daga lokaci zuwa lokaci, domin tabbatar da ganin ya yi daidai da wanda tsarin doka ta tanada.

Sai dai ya zama wajibi irin wannan manufa ta sarrafa kudaden shiga ya kasance wadda majalisar dokoki ta tarayya ta amince da ita.