Home Labaru Kisan Kolade: Shugaba Buhari Ya Ce Za A Hukunta ‘Yan Sandan Da...

Kisan Kolade: Shugaba Buhari Ya Ce Za A Hukunta ‘Yan Sandan Da Ke Da Hannu A Ciki

393
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta dauki kwakkwaran mataki a kan ‘yan sandan da su ka kashe Kolade Johnson.

Buhari ya bayyana rashin jin dadin shi, sannan ya yi Allah-wadai da irin matakin da rundunar ‘yan sandan ‘SARS’ ta dauka, wanda har ya yi sanadiyyar mutuwar Kolade Johnson.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya fitar, ya nuna rashin jin dadin sa game da abin da rundunar ‘yan sanda na SARS ta yi.

Shugaban Buhari, ya ce gwamnati ba za ta taba yarda da wata hanya da za a rika cin zarafin ‘yan Nijeriya ba, kuma duk wani jami’in tsaro ko ma’aikacin gwamnati da aka kama ya na cin zarafin wani a Nijeriya zai fuskanci hukunci mai tsanani.Yanzu haka dai wadanda ake zargin sun shiga hannu, sannan nan ba da dadewa ba za a gabatar da su a gaban kotu domin yanke masu hukunci.

Leave a Reply