Home Labaru Shugabancin Majalisa: Sanata Ndume Ya Yi Biris Da Umurnin Jam’iyyar APC

Shugabancin Majalisa: Sanata Ndume Ya Yi Biris Da Umurnin Jam’iyyar APC

334
0
Sanata Ali Ndume, Dan Majalisar Dattawa
Sanata Ali Ndume, Dan Majalisar Dattawa

Dan majalisar dattawa Sanata Ali Ndume, ya yi watsi da umarnin da shugabannin jam’iyyar APC su ka bada, cewa Sanata Ahmed Lawan ne zai zama Shugaban Majalisar Dattawa.

Tuni dai Sanatan ya fitar da daftarin kudirorin sa guda 9, wadanda ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa a kan su ne zai tafiyar da jagoranci.

Ndume ya ce bai amince a hana shi takara ba, domin shugaban jam’iyyar APC ne ya tsaida Lawan ba tare da tuntubar kowa ba. Daga cikin kudirorin Sanata Ndume kuwa akwai yin aiki kafada da kafada da gwamnati ba tare da yi wa juna katsalandan ba, da kuma rage kwarjinin shugabancin majalisa ta yadda za a rage rububin neman matsayin.