Home Labaru Tattalin Arziki: Nijeriya Na Daya Daga Cikin Kasashen Da Ba A Bin...

Tattalin Arziki: Nijeriya Na Daya Daga Cikin Kasashen Da Ba A Bin Su Bashi Sosai A Duniya – Osinbajo

282
0
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Nijeriya ta na daya daga cikin kasashen da ba a bin su bashi da yawa a fadin duniya

Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce yanzu haka Nijeriya ce kasar da ake bin ta bashi mafi karanci a fadin duniya.

Osinbajo ya bayyana haka ne, a lokacin da ya ke bayani a wani taro da ya halarta a jami’ar Lagos da ke Akoka, inda ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta yi kokari wajen farfado da tattalin arzikin Nijeriya a shekaru hudu da su ka gabata.

Ya ce sun yi bakin kokarin su wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan, saboda a halin yanzu cikin kashi 100 bai fi kashi 22 ake bin Nijeriya ba, kuma a yanzu bashin Nijeriya ya na daya daga cikin mafi karanci da ake bin kasashen duniya.