Home Labaru Kisan Fararen Hula: Rundunar Sojin Sama Ta Maida Wa Sarakunan Zamfara Martani

Kisan Fararen Hula: Rundunar Sojin Sama Ta Maida Wa Sarakunan Zamfara Martani

733
0

Rundunar sojin sama ta Nijeriya, ta maida martani a kan fitar da jerin sunayen mutanen da sarakunan jihar Zamfara su ka zarge ta da kashewa yayin wani luguden wuta da ta yi a sansanin ‘yan bidigar da su ka addabi jihar.

Kungiyar sarakunan jihar Zamfara ta hannun shugaban ta sarkin Bungudu Alhaji Hassan Attahiru, ta fitar da wani jerin sunayen fararen hula da ta yi zargin cewa rundunar sojin ce ta kashe su yayin wani samame ta sararin samaniya.

Bayan sakin sunayen mutanen, shugaban rundunar sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar, ya kafa kwamitin bincike a karkashin mataimakin sa, wanda zai bi diddigi a kan zargin da sarakunan su ka yi.

A wata zantawa da ya yi manema labarai a Abuja, daraktan yada labarai da hulda da jama’a na rundunar Kwamado Ibikunle Daramola, ya yi watsi tare da karyata zargin cewa rundunar ta yi amfani da bom a jihar Zamfara.

Ya ce duk da rundunar za ta gudanar da bincike a kan duk sunayen da sarakunan su ka fitar, dakarun rundunar ba za su tsagaita da aikin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al’umma a jihar Zamfara ba.

Leave a Reply