Wata kotun tarayya da ke zaman a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi, ta tsige dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Ebonyi ta kudu Sanata Sonni Ogbuoji, saboda ya sauya sheka daga jam’iyyar da aka zabe shi zuwa wata.
Yanzu haka dai kujerar sanatan jihar Ebonyi ta kudu a majalisar dattawa ta na matsayin wadda babu kowa a kan ta, biyo bayan hukuncin kotun da ya tsige Sanata Ogbuoji.
Idan dai za a iya tunawa, an zabi Sanata Ogbuoji ne a karkashin jam’iyyar PDP, amma ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a shekara ta 2018.
Kotun, ta kuma ba hukumar zabe ta kasa umurnin karbe shahadar cin zabe, sannan ta gudanar da sabon zabe cikin gaugawa domin maye gurbin Sanata Ogbuoji.
Alkalin kotun mai shari’a Akintola Aluko, ya ce sauyin shekar Ogbuoji ya saba wa sashe na 68 (1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekara ta 1999, wanda ya ce duk dan majalisar da ya sauya sheka daga jam’iyyar da aka zabe shi kafin karewar wa’adin sa zai bar kujerar sa.
You must log in to post a comment.