Majalisar dokoki ta jihar Kaduna, ta kawo kudirin da zai kawo gyara wajen harkar bizne gawa a fadin jihar, inda za a rika yi wa kowace gawa rajista kafin a bizne ta a cikin makabarta.
Kamar yadda su ka ruwaito, kudirin zai ba kananan hukumomi dama karber makabartun jihar, sannan su rika bada takardar izinin bizne gawa a duk lokacin da aka rasu.
Mataimakin shugaban majalisar dokoki ta jihar Kaduna Nuhu Shadalafiya ne ya jagoranci zaman da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata, inda mafi yawan ‘yan majalisar su ka amince da wannan kudiri.
Shadalafiya, ya ce idan kudirin ya zama doka, zai ba kananan hukumomin jihar Kaduna ikon ware kudin gina makabartu da katangewa da daukar nauyi da kuma kula da batun tsaro da sha’anin ma’aikata.
An dai amince da kudiri ne, bayan kwamitin da ya yi aikin ya gabatar da rahoton sa a zauren majalisar.
Kudirin zai haramta wa jama’a bizne gawa a wuraren zaman al’umma, kuma za a ci duk wanda ya saba wa dokar tarar Naira 50, 000.
You must log in to post a comment.