Majalisar dattawa ta janye sa hannu a kan kasafin shekara ta 2019 zuwa mako mai zuwa saboda rashin samun cikakkun bayanai.
A ranar Alhamis din nan ne, kwamitin kasafi na majalisar Dattawa a karkashin jagorancin Sanata Danjuma Goje ya gabatar da kudurin kasafin.
Sai dai a lokacin da majalisar ta zauna a kan lamarin, sun gano cewa babu cikakkun bayanai game da kasafin kudin.
Haka kuma, sun lura cewa shugaban kwamitin Sanata Danjuma Goje da mataimakin sa Sanata Sunny Ogbouji ba su halarci zaman ba, amma babban dalilin jinkir ta kasafin shi ne rashin samun cikakkun bayanai.
Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, ya bukaci a tanadi bayanan kasafin kafin ranar Litinin mai zuwa, saboda majalisar ta sanya hannu a kan shi ranar Talata mai zuwa.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun matsala a kan gabatar da kasafi a Nijeriya ba, musamman tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari a kan kujerar mulki.