Home Labaru Shugabanci: Osinbajo Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa A Abuja

Shugabanci: Osinbajo Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa A Abuja

238
0

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta tarayya a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Wata majiya ta ce, an fara taron ne, jim kadan bayan isar mataimakin Shugaban kasa zauren majalisar da ke fadar Shugaban kasa da misalin karfe 11:00 na rana.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da shugabar ma’aikatan tarayya Wanifred Oyo-Ita da ministoci 20 ne su ka hallarci zaman, yayin da aka hana ‘yan jarida shiga dakin taron.

Idan dai za a iya tunawa, Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Birtaniya a ranar Alhamis din nan, bayan ya ziyarci Maiduguri kamar yadda mai Magana da yawun say a bayyana.

Leave a Reply