Home Labaru Boko Haram: Gwamnatin Nijeriya Ta Nemi Kasar Rasha Ta Kawo Mata Dauki

Boko Haram: Gwamnatin Nijeriya Ta Nemi Kasar Rasha Ta Kawo Mata Dauki

294
0

Gwamnatin tarayya ta nemi agajin kasar Rasha domin kawo karshen ta’addancin kungiyar Boko Haram, musamman a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya da gabar tafkin Chadi.

Ministan tsaro Mansur Dan Ali ya mika kokon barar, yayin halartar taron tsaro na duniya karo na takwas da aka gudanar a birnin Moscow na kasar Rasha a ranar Larabar da ta gabata.

Ministan, ya kuma nemi hadin gwiwar kasar Rasha wajen bada gudumuwar kariya ga yankunan teku na Nijeriya da ke gabar tsuburin kasar Guinea.

Yayin lura da kwarewar kasar Rasha wajen gudanar da harkokin yaki da ta,addanci, Dan Ali ya nemi kasar ta kawo wa Nijeriya daukin kawo karshen ta’addanci Boko Haram a fadin kasar nan.

Ministan ya kuma bayyana damuwa, game da yadda ta’addanci ke ci-gaba da tsananta a nahiyyar Afirka, inda ya yi misali musamman da kungiyoyi masu tada kayar baya na Boko Haram da kungiyar Al-Shabaab da kuma kungiyar ISIS.

Leave a Reply