Gwamnatin tarayya, ta bayyana damuwa a kan adadin ‘yan Nijeriya da ke zaman jiran hukunci da wadanda aka zartar masu da hukuncin kisa a kasar Saudiya sakamakon laifuffukan da su ka shafi fataucin miyagun kwayoyi.
Wata majiya ta ce, gwamnati na neman a sassauta wa ‘yan Nijeriya hukuncin kisa da hukumomin kasar Saudiya su ka zartar a kan su.
Babbar mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin ketare Abike Dabiri ta bayyana haka, yayin wata hira da manema labarai na fadar shugaban kasa da ke Abuja. A ranar Litinin din da ta gabata ne, gwamnatin kasar Saudiya ta salwantar da rayuka bayan tabbatar da hukunci na haddin kisa a kan wasu Maza biyu ‘yan kasar Pakistan da wata Mata ‘yar Najeriya saboda laifin fataucin miyagun kwayoyi da su ka aikata.
You must log in to post a comment.