Home Labaru Ilimi Kammala Karatun Jami’a Na Bogi: JAMB Ta Bankaɗo Ɗalibai 3000

Kammala Karatun Jami’a Na Bogi: JAMB Ta Bankaɗo Ɗalibai 3000

18
0
Official JAMB logo
Official JAMB logo

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta ƙasa (JAMB) a Najeriya ta bankaɗo daliban da suka kammala karatun jami’a na bogi 3,000,

da kuma mallakar takardun shaidar kammala karatu ba bisa ƙa’ida ba a duk faɗin ƙasar.

Magatakardar hukumar, farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan kuma ya ce waɗannan mutane ba su taɓa zuwa jami’a ba,

wanda hakan ya nuna irin cin hanci da rashawa da ake samu a harkar ilimi.

Oloyede ya soki yadda wasu cibiyoyin karatu suke shigar da ɗalibai makarantu ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa abin kunya ne ga al’ummar ƙasar.

Ya kuma buƙaci kwamitin Pro-Chancellor na Jami’o’in Jihohi a Najeriya (COPSUN) da su yaƙi irin waɗannan ayyuka.

A watan Disamban 2023, Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimin Farko ya buƙaci Hukumar JAMB ta samar da jerin sunayen cibiyoyin da ke da hannu wajen shigar da ɗaliban jami’o’i ba bisa ƙa’ida ba.

Leave a Reply