Home Labarai Matsalar Tsaro: Malaman Jami’ar Dutsinma Sun Yi Zanga-Zanga

Matsalar Tsaro: Malaman Jami’ar Dutsinma Sun Yi Zanga-Zanga

15
0
bandit
bandit

Malaman Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke garin Dutsin-Ma a jihar Katsina sun gudanar da zanga-zanga a harabar jami’ar kan matsalar tsaro.

Zanga-zangar wadda mukaddashin shugaban ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) reshen jami’ar tarayya da ke Dutsin-Ma, Kwamared Dahiru Rabe ya jagoranta,

ta koka ne kan yadda matsalar sace-sacen jama’a ke karuwa a Dutsin-Ma, wanda ke shafan ma’aikatan jami’ar.

A watan da ya gabata ne aka yi garkuwa da ma’aikatan jami’ar biyu da kuma yaron wani malamin jami’ar.

A ranar Litinin din da ta gabata kuma, an kai wa wani ma’aikacin jami’ar hari tare da kashe shi da kuma yin garkuwa da ‘ya’yan sa maza biyu tare da wata daliba da diyar ta.

Leave a Reply