Home Labarai Yarjejeniyar SAMOA: Majalisar Wakilan Najeriya Ta Nemi A Dakata

Yarjejeniyar SAMOA: Majalisar Wakilan Najeriya Ta Nemi A Dakata

207
0
House of reps2 900x563
House of reps2 900x563

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta dakatar da yarjejeniyar Samoa da ta tayar da ƙura a kasar.

A zaman da ta yi yau Talata, majalisar ta ce ya kamata a dakatar da yarjejeniyar har sai gwamnati ta fito ta bayyana ɓangarorin yarjejeniyar da suka haifar da cecekuce.

Ɗan majalisar wakilai Hon Aliyu Madaki, ya ce majalisar ta kuma nemi ministocin da suka jagoranci sanya hannu a yarjejeniyar

su gurfana gabanta tare da takardun yarjejeniyar domin buƙatar fayyace komi musamman “ɓangaren dake bayani kan daidaiton jinsi.

Yarjejeniyar Samoa da gwamnatin Najeriya ta sanya wa hannu da tarayyar Turai ta tayar da ƙura a Najeriya inda wasu ƴan ƙasar nan da dama suka nuna fushinsu

musamman zargin cewa yarjejeniyar na ƙunshe da wani ɓangare da ke nuna goyon baya da kuma kare muradun masu maɗigo da luwaɗi.

Sai dai tuni gwamnatin Najeriya ta musanta, inda ministan kasafin kudi da tsare-tsare da kuma ministan watsa

labarai suka ce Najeriya ba za ta taɓa amincewa da wata yarjejeniyar da ta saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar nan da kuma al’adu da addinin ƙasar.

Leave a Reply