Home Labaru Inganta Kiwo: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Kidayar Dabbobi Da Kuma Yi Masu...

Inganta Kiwo: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Kidayar Dabbobi Da Kuma Yi Masu Shaida

356
0

Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da kidaya da tantancewa tare da sanya wa dabbobin kiwon shaida a fadin Nijeriya.

Babban sakataren dindindin na ma’aikatar noma da raya karkara ta kasa Dakta Muhammad Bello Umar ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Babban sakataren dindindin na ma’aikatar noma da raya karkara ta kasa

A cewar sa, yunkurin zai taimaka tare da taka muhimmiyar rawar gani wajen magance dabi’ar satar dabbobi da kuma samun ainihin adadin dabbobin kiwo da ke fadin  kasar nan.

Shugaban cibiyar kula da lafiyar dabbobi Bright Wategire ne ya wakilci babban sakataren a wajen taron kara wa juna sani da aka gudanar game da muhimmancin kidayar dabbobi da kuma tantancewa.

Bright, ya ce a halin yanzu saura kiris gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen ta na shimfida dokokin samarwa da kuma mallakar shanun kiwo.