Shahararren malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi, ya fara tuntubar manyan Nijeriya domin su sa baki tare da yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya saki shugaban ‘yan shi’a Ibrahim Zakzaky.
Sheikh Gumi ya yi wannan yunkuri ne, duba da irin tarzomar da lamarin ke janyowa a birnin tarayya Abuja, da kuma gudun abin da ka iya faruwa nan gaba idan har gwamnati ta cigaba da rike El-Zakzakky.

Wata majiya ta ce, a kokarin ganin an shawo kan matsalar, Sheikh Ahmad Gumi ya yi tattaki zuwa gidan jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu, inda ya bukaci ya yi wa shugaba Buhari magana ya saki El-Zakzaky.
Majiyar ta cigaba da cewa, bayan sauraren jawabin malamin, Tinubu ya ba shi tabbaci tare da alkawarin zai isar da sakon sa ga shugaba Muhammadu Buhari.
Idan dai za a iya tunawa, a baya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya taba yin kira ga shugaba Muhammadu Buhahri ya duba lamarin Ibrahim El-Zakzakky.
You must log in to post a comment.