Home Labaru Hukumar Raba Daidai Ta Nijeriya Ta Bukaci A Kara Wa Tinubu Da...

Hukumar Raba Daidai Ta Nijeriya Ta Bukaci A Kara Wa Tinubu Da Gwamoni Albashi

108
0

Shugaban kasa mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu, zai cigaba
da karbar Naira miliyan 1 da dubu dari biyu a matsayin
albashi sa duk wata kamar yadda shugaba Muhammadu
Buhari ya ke karba.

Tunibu dai zai cigaba da karbar albashin a haka idan har ba a sanya hannu a kan kudurin karin albashin masu rike da mukaman siyasa da manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya ya zama doka ba.

Babban shugaban hukumar raba daidai na kasa Dakta Bello Muhammad Shehu ya bayyana haka, a wani taron lakca karo na farko a kan tattalin arziki da gabatar da wani Littafi a Abuja.

Dakta Bello, ya ce gwamnoni su na karbar Naira miliyan 1 da dubu 100 a matsayin albashi duk wata, ya na mai cewa, wasu manyan ma’aikatan hukomomin gwamnatin tarayya su na karbar albashin da ya dara na shugaban kasa da gwamnoni.

Ya ce Shugaban kasa ya na karbar albashin Naira miliyan 1 da dubu 200 ne duk wata, kuma ya na da tabbacin cewa wasu manya a hukomomin gwamnatin tarayya su na karbar albashin Naira miliyan 5 wasu kuma Naira miliyan 2.

Leave a Reply